Matsalar tsaro da corona sun addabi Kamaru gab da gasar cin kofin Afrika
Yayinda kasar Kamaru ta kammala dukkan shirye-shirye don fara wasannin gasar cin kofin Afrika da za a fara Lahadi mai zuwa, na tsawon wata daya, har yanzu akwai fargabar yadda za ta kasance saboda matsalolin rashin tsaro a kasar.
Wallafawa ranar:
Wadanda za su bude wannan gasa a ranar lahadi mai zuwa dai akwai Kamaru, mai masaukin baki da za ta kara da Burkina Faso.
Kasar ta Kamaru dai na fama da annobar hare-haren ‘yan awaren yammaci, ga kuma masu jihadi da karfin tsiya a gabashin kasar, al’amurran da ake fargaban kada ‘yan ta'addan su yi amfani da damar wasannin su kaddamar da hare-haren nasu.
Jami'an tsaro a kasar na cikin shirin ko ta kwana, bayanda aka sami wasu kungiyoyin ‘yan ta'addan na aikewa da sakonnin da ke barazana ga tarukan da za a yi.
Kungiyoyin wasan na rukunin F wato na shida, da suka hada da Tunusia, Mali, Mauritania da Gambia ne dai suka sami sakonnina barazana ga ‘yan wasansu.
Wasannin da wadannan kasashen hudu za su yi ne a garin Limbe kuma suna motsa jiki ne a Buea masu hadarin gaske saboda rashin tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu