Isa ga babban shafi
Mali-Keita

Al'ummar Mali sun fara makokin shugaba Ibrahim Boubacar Keita

Mali ta fara makokin tsohon shugabanta Ibrahim Boubacar Keita da ya mutu jiya lahadi ya na da shekaru 76, rasuwar da ke zuwa shekaru 2 bayan hambarar da gwamnatinsa da Sojoji suka yi a watan Agustan 2020.

Tsohon Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita
Tsohon Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita Ludovic Marin /Pool via REUTERS
Talla

Tsohon shugaban na Mali da ya mulki kasar mai yawan jama’a miliyan 19 daga 2013 gabanin hambarar da kujerarsa a watan Agustan 2020 bayanai daga iyalansa sun ce ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Sanawar da gwamnatin Sojin Mali ta fitar ta bayyana Keita a jerin zakakuran shugabanni da Mali ta gani a tarihi yayinda ta aike da ta’aziyyar shugaban wanda ta ce ya rasu sakamakon doguwar jinya da ya yi, ko da ya ke bata fayyace nau’in cutar da tsohon shugaban ya yi fama da ita ba ko kuma tsawon lokacin da ya dauka.

Tuni dai shugabannin kasashe suka fara aike da sakon gaisuwa ga rashin na Boubacar Keita da ake yiwa lakabi IBK, ciki har da Macky Sall na Senegal da tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou wadanda suka bayyana Keita a matsayin jajirtacce da ya yi shurab wajen tabbatar da zaman lafiya.

Ayyukan ta’addancin mayaka masu ikirarin jihadi da rikicin kabilanci da kuma durkushewar tattalin arziki sun haddasa babban nakasu ga gwamnatin Keita a kasar mai fama da matsanancin talauci gabanin zabensa na 2019 da ya jefa Mali a rikicin siyasa, yayinda kuma badakalar dan shugaban Karim Keita ta sake rura kiyayya ga Keita.

Haka zalika garkuwa da jagoran adawar kasar Soumaila Cisse a cikin watan Maris din 2020 gabanin mutuwarsa a watan Disamba sakamakon harbuwa da corona ya sake assasa rikicin kasar.

Bayan jerin bore daga al’ummar kasar sakamakon tsanantar suka daga bangaren adawa ne Sojoji suka yi juyin mulki ga shugaba Keita da nufin kawo karshen zub da jinin.

Rikicin Mali tsohuwar diyar goyon Faransa ya hallaka dubunnan rayuwa yayinda miliyoyi suka rasa matsugunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.