Isa ga babban shafi
Mali-Rasha-Faransa

Rashin jituwa ya sake tsananta tsakanin Sojojin Mali da Faransa

Faransa na kara azama wajen tattaunawa da kawayenta na Turai a game da dambarwar da ke tsakaninta da kasar Mali da ke fama da tashin hankali, wadda ke barazanar rikidewa zuwa rikici tsakaninta da gwamnatin sojin Bamako.

Kanar Assimi Goita da ke jagorancin gwamnatin Soji a Mali.
Kanar Assimi Goita da ke jagorancin gwamnatin Soji a Mali. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

A shekarar 2020 ne Faransa  ta kafa rundunar hadin gwiwa ta Takuba, da zummar jan hankalin kawayenta na Turai wajen daukar wani bangare na nauyin yaki da ta’addanci a Mali.

An samar da gamayyar, wadda ta tattaro dakaru na musamman  daga kasashen Turai a karkashin jagorancin Faransa don  bada shawarwari ga sojojin Mali, tare da taimaka musu a fagen daga.

Al’amuran da suka auku a baya bayan sun sa dakarun Takuba sun karu zuwa dari 9, amma makomar aikin na samun cikas sakamakon gutsiri   tsoma tsakanin Faransa da Mali.

Rikicin da ya kunno kai tun bayan juyin mulkin Mali na watan Agusta ya zafafa, musamman tun da sojojin Mali din suka sanar da dauko sojojin haya daga Russia, matakin da Faransa ta nuna ba ta so.

Matsalar  baya bayan nan ya kunno kai ne lokacin da Mali ta bukaci dakarun Denmark da suka sauka kasar don aikin rundunar Takuba su koma, bisa dalilin cewa an gayyato su ba da saninta ba.

Ministar Tsaron Faransa  Florence Parly ta caccaki wannan mataki, wanda ke zuwa mako guda bayan Mali ta nemi a sake nazarta yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasashen 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.