Isa ga babban shafi
Mali

Sojojin Mali sun bukaci Denmark ta gaggauta janye dakarunta daga kasar

Gwamnatin sojin Mali ta bukaci Denmark da ta gaggauta janye sojojinta da ta tura zuwa yankin yammacin Afirka a matsayin wani bangare na rundunar yaki da ta'addanci ta Takuba da Faransa ke jagoranta, saboda ba a tuntube ta ba, sannan kasar ta Denmark ta gaza bin ka'ida.

Shugaban gwamnatin sojojin kasar Mali Kanal Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin sojojin kasar Mali Kanal Assimi Goita. © Nipah Dennis / AFP
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Mali ta bayyana mamakin ganin yadda ba tare da neman izininta ba, Denmark ta jibge dakarunta na musamman zuwa sabuwar rundunar Takuba da ta kunshi dakarun wasu daga cikin manyan kasashen Turai a garin Menaka da ke kasar ta Mali, dan haka ya kamata a janye sojojin na Danish cikin gaggawa.

Sanarwar ta ce dukkan abokan huldar rundunar na bukatar tuntubar juna da gwamnati kafin tura sojoji zuwa Mali.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun saka tsakanin kasar Mali da kawayenta na kasa da kasa da suka hada da kungiyar ECOWAS, da kuma kungiyar Tarayyar Turai da suka sanyawa Mali takunkumi bayan da gwamnatin rikon kwarya ta ki shirya zabe a watan Fabarairu, bayan juyin mulkin soji har guda biyu.

Tsamin dangantakar tsakanin Mali da kasashen na ECOWAS da Turai ne, bayan zargin cewa gwamnatin sojin kasar sun kulla yarjejeniya da kamfanin bayar da sojojin haya na Wagner da ke samun goyon bayan gwamnatin Rasha, matakin da wasu kasashen Tarayyar Turai suka yi tir da shi.

A makon da ya gabata ma'aikatar tsaron Denmark ta bayyana tura sojoji da sauran ma’aikata akalla 90, da suka hada da likitocin fida da sojojin musamman da tallafin kayan aiki,  domin taimakawa wajen yaki da ta’addanci a Mali har zuwa farkon shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.