Sojan Faransa na 53 ya mutu a yankin Gao na kasar Mali
Wani sojan Faransa ya rasa ran sa a jiya asabar a kasar Mali bayan wani harin da manyan bindigogi da aka kai bariqin sojojin Barkhane dake garin Gao. Sanarwar da fadar Shugaban Faransa ta Elysee ta bayar na nuna cewa Shugaban kasar Emmanuel Macron cikin kaduwa ya bayyana jimamen sa tareda isar da ta’aziya ga iyalan mammacin Birgaidiya Alexandre Martin dake aiki da rundunar artillery ta 54.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Faransa ta bayyana cewa babu gudu ba ja da baya za ta ci gaba da yakin da take da yan ta’adda tare da goyan bayan kawayan ta a Sahel.
Da misalign karfe biyar na yammacin jiya ne aka yi ta jin harbi da manyan makamai zuwa bariqin sojojin barkhane dake yankin na Gao a cewar mai magana da yahun rundunar tsaron Faransa Kanal Pascal Ianni.
Kanal Pascal ya karasa da cewa nan take,aka tayar da jirage masu saukar ungulu da nufin murkushe maharani,nasar da suka samu ba tare da bata lokaci ba.Wannan dai ne sojan Faransa na 53 dake rasa ran sa a kasar ta Mali tun bayan shigar Faransa yakin a shekara ta 2013
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu