Isa ga babban shafi

Kasar Mali ta hana jirgin sojin Jamus ratsa sararin samaniyarta

Mali ta hana wa wani jirgin sojin kasar Jamus izinin ratsa sararin samaniyarta a yammacin jiya laraba, lamarin da ya tislata wa jirgin mai dauke da sojoji 75 sauka a tsibirin Canaria na kasar Spain.

Kasar Mali
Kasar Mali Eléonore HUGHES AFP
Talla

A farkon watan Janairu ne Taron shugabannin kasashen yankin yammacin Afrika Ecowas/Cedeao, ya amince da sanya wa Mali sabbin takunkumai don tilasta wa sojoji gaggauta mika mulkin kasar a hannun zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya.

Yankin Sahel
Yankin Sahel © (AP Photo/Sam Mednick)

Har ila yau taron,wanda ya hada da kungiyoyi biyu,wato Ecowas da kuma  Uemoa wato kungiyar kasashe masu amfani da takardar kudin Cfa,ya ce daga yanzu an haramta duk wata hada-hadar kudade tsakanin Mali da sauran kasashen yankin 14.

Wannan al’amari ya tilastawa hukumomin Mali daukar wasu matakai na hana jirage ratsa sararin samaniyarta.

Daya daga cikin jirgin jigilar sojin  Faransa
Daya daga cikin jirgin jigilar sojin Faransa © RFI/Franck Alexandre

Mai magana da yawun rundunar sojin Jamus, ya ce jirgin wanda ke dauke da sojoji da kuma kayan aiki, yana hanyarsa ta zuwa birnin Yamai na jamhuriyar Nijar ne.

Jamus dai na da dakaru 1.200 a yankin Sahel, wadanda wa’adin aikinsu zai kawo karshe a watan mayu tare da yiyuwar tsawaita wa’adin aikin nasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.