Isa ga babban shafi

DRC-'Yan bindiga sun hallaka mutane 40 a sansanin 'yan gudun hijira

Majiyoyi a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun ce wasu ‘Yan bindiga sun kai hari a sansanin mutanen da aka raba da matsugunin su dake gabashin kasar inda suka kashe akalla mutane 40.

Yankin Lita dake Lendu a DRCongo
Yankin Lita dake Lendu a DRCongo ALEX MCBRIDE / AFP
Talla

Kungiyar dake sanya ido a Yankin Kivu tace ‘Yan bindigar sun kai harin da wukake ne daren jiya inda suka hallaka mutanen a Plaine Savo.Jami’an yankin da kungiyoyin fararen hula sun ce adadin wadanda aka kashe ya zarce 50, yayin da kakakin sojin yankin Ituri Laftanar Jules Ngongo yace sun tabbatar da mutuwar mutane 21 ne.

Daya daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a DRCongo
Daya daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a DRCongo Racove, Radio communautaire de la Vérité

Kungiyar dake sanya ido akan rikicin yankin tace wata kungiyar ‘Yan bindiga da ake kira CODECO ce ta kai harin, wanda ta danganta shi da kisan kabilanci da ake fama da shi a wurin.

Al'umar yankin Goma na DRCongo yayin rijistan masu zabe
Al'umar yankin Goma na DRCongo yayin rijistan masu zabe Guerchom Ndebo AFP

‘Yankin Djugu dake iyaka da Tafkin Albert da kuma kasar Uganda ya zama wani dandalin zubda jini na dogon lokaci tsakanin ‘Yan kabilar Lendu da Hema. Fada tsakanin wadannan al’ummomi ya barke ne tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003, inda ya lakume rayukan dubban mutane kafin dakarun kasashen Turai su shawo kan sa ta hanyar aikin samar da zaman lafiya.

Taswirar DRCongo
Taswirar DRCongo Vincent LEFAI AFP/File

Daga bisani tashin hankalin ya sake dawowa a shekarar 2017 wanda ake zargin kungiyar CODECO da haifarwa abinda ya kaiga kai hari akan mutanen da suka rasa matsugunan sun a kwanaki 8 tsakanin watan Nuwamba da Disambar da ta gabata, ya kuma yi sanadiyar kashe mutane 123.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.