Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Masu shigar da kara a Burkina Faso na son a daure Compaore na shekaru 30

Masu gabatar da kara na soji a kasar Burkina Faso sun bukaci yankewa tsohon shugaban kasa Blaise Compaore hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari saboda zargin da ake masa na hannu wajen kashe shugaban juyin juya hali Thomas Sankara a shekarar 1987.

Hambararren shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore.
Hambararren shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Ana yiwa Compaore shari’ar ce a bayan idan sa saboda tserewa kaasr Cote d’Ivoire da yayi inda ya samu mafaka a shekarar 2014.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 1 ga watan Maris kamar yadda masu kare Compaore suka bukata.

'Yan Afirka na kallon Sankara a matsayin gwarzo saboda sauye sauyen da ya gabatar a kasar bayan hawa karagar mulki a shekarar 1983 lokacin yana da shekaru 33 a duniya a matsayin Kaftin din soja.

A ranar 15 ga watan Oktobar shekarar 1987 sojoji suka hallaka shi tare da wasu jami’an gwamnatin sa 12 lokacin da suke halartar taron majalisar ministoci.

Bayan kasha Sankara, Compaore yah au karagar mulki inda ya jagoranci Burkina Faso na shekaru 27 har zuwa shekarar 2014 da zanga zangar jama’ar kasar ta tilasta masa tserewa zuwa kasar Cote d’Ivoire.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.