Isa ga babban shafi
Benin-Ta'addanci

Harin ta'addanci ya hallaka jami'an tsaron Benin 6 a gandun dajin kasar

Akalla jami’an tsaron gandun daji 5 da kuma Soji guda ne suka rasa ransu yayin wani harin mayaka masu ikirarin jihadi a babban gandun dajin Arewacin Benin da ke gab da iyakar kasar da Burkina Faso da Jamhuriyyar Nijar.

Wani yankin na gandun dajin da ke arewacin Benin.
Wani yankin na gandun dajin da ke arewacin Benin. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Ma’aikatar kula da gandun dajin na Benin da ke tabbatar da harin ta ce akwai kuma wasu mutum 10 da suka samu raunuka a farmakin wanda har zuwa yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kaddamar da shi.

Hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi dai daga yankin Sahel a baya-bayan ya fara fantsama zuwa sassan arewacin kasar ta Benin da ke yammacin Afrika mai iyaka da gabar teku.

Acewar ma’aikatar farmakin ya faru ne a jiya labarai lokacin da jami’an tsaron ke rangadi a cikin gandun dajin wanda ya yi iyaka da wasu yankuna na Burkina Faso da Nijar.

Gandun dajin wanda tun shekarar 2020 ke karkashin kulawar ma’aikatar tsaro mai zaman kanta, tuni aka aike da wasu karun dakaru yankin da al’amarin ya faru don kakkabe barazanar da ke kunno kai.

Dama ma’aikatar tsaron Benin ta girke karin dakaru a yankin arewaci tun bayan samun harin ta’addanci sau 2 cikin shekarar 2021 irinsa na farko da kasar ta gani.

Ko a watan jiya, dakarun sojin Benin 2 sun kwanta dama bayan da motarsu ta taka wata birnanniyar nakiya a yankin Atakora da ke arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.