Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Sojin Mali sun kashe 'yan ta'adda 57 yayin farmaki kan maboyarsu

Rundunar Sojin Mali ta sanar da kashe 'yan ta'adda 57 yayin sumamen dakarunta a yankin arewa maso gabashin Archam mai fama da hare-haren ta'addanci.

Wasu dakarun Sojin Mali da suka samu horo karkashin kulawar Sojojin hayar kamfanin Wagner na Rasha.
Wasu dakarun Sojin Mali da suka samu horo karkashin kulawar Sojojin hayar kamfanin Wagner na Rasha. FLORENT VERGNES AFP
Talla

Sanarwar ta ma’aikatar tsaron Mali ta fitar ta ce yayin sumamen dakarunta 8 sun kwanta dama yayinda wasu 5 suka yi batan dabo a cikin daji.

Sumamen Sojin dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Faransa ta sanar da aniyar janye dakarunta baki daya daga kasar ta Sahel mai fama da hare-haren ta’addanci.

Haka zalika farmakin Sojin ya zo ne kwana guda bayan harin mayaka masu ikirarin jihadi da ya kashe fararen hula kusan 40 a tsakiyar kasar.

Hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi na ci gaba da tsananta a kasar ta Mali da ke yankin Sahel dai dai lokacin da dakarun ketare da ke taimakawa kasar yakar ayyukan ta'addanci ke gab da ficewa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.