Isa ga babban shafi
Amurka - Burkina Faso

Amurka ta dakatar da tallafin kusan dala miliyan 160 ga Burkina Faso

Amurka ta dakatar da tallafin kusan dala miliyan 160 da take baiwa Burkina Faso, bayan da ta tabbatar da hambarar da shugaba Roch Kabore a watan Janairu, a matsayin juyin mulkin soji.

Laftanar Kanal Paul-Henri Damiba, jagoran sojojin Burkina Faso da suka yi juyin mulki.
Laftanar Kanal Paul-Henri Damiba, jagoran sojojin Burkina Faso da suka yi juyin mulki. via REUTERS - Burkina Faso Presidency Press Se
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar da daukar matakin ne, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Juma’ar da ta gabata.

Gwamnatin Amurkan ta ce ta yanke shawarar daukar matakin ne a karkashin dokar da ta fayyace dakatar da tallafin da Amurka ke bayarwa don inganta dimokuradiyya ga kasar da aka hambarar da zababben shugaba ta hanyar juyin mulkin soja, ko kuma juyin mulkin da sojoji suka taka muhimmiyar rawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.