Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

Majalisar Mali ta amince sojoji su mulki kasar

‘Yan Majalisar Dokokin Mali sun amince da wani kudirin doka da zai bai wa sojoji damar shugabancin kasar har tsawon shekaru biyar masu zuwa, duk da takunkuman da aka kakaba wa kasar sakamakon jinkirta gudanar da zabe.

Jagoran mulkin sojin Mali, Assimi Goïta.
Jagoran mulkin sojin Mali, Assimi Goïta. REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

Tun bayan da suka karbe mulki a cikin watan Agustan 2020, sojojin Mali suka yi alkawarin gudanar da zabe a cikin watan Fabirun wannan shekara a kasar da ke yankin Sahel.

Sai dai a cikin watan Disamban da ya gabata, sojojin suka bukaci ci gaba da kankamewa kan karaga tsakanin watanni shida zuwa shekara biyar, suna masu kafa hujja da matsalar tsaro.

Tuni  Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta lafta jerin takunkumai kan Mali a matsayin martini, inda ta kuma rufe kan iyakokin kasar.

ECOWAS ta kuma yi watsi da matakin sojojin na tsawaita zamansu kan karagar mulkin kasar.

A wannan Litinin ne, mambobin rikon kwarya a majalisar dokokin Malin 120 daga cikin 121 suka kada kuri’ar amince wa sojojin ci gaba da mulki har zuwa shekaru biyar nan gaba, abin da ya yi daidai da bukatar da sojojin suka gabatar tun a can baya.

Sannan babu wani bayani game da takamammiyar ranar da za a gudanar da zabe koda shekaru biyar din sun cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.