Isa ga babban shafi
Mali

Sojojin Mali da na Turai sun kashe ‘yan ta’adda 19

Sojojin Mali sun sanar da kashe mayakan ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi 19, a wani samame da suka kai a yankin arewa maso gabas da Bamako babban birnin kasar.

Wasu sojojin kasar Mali.
Wasu sojojin kasar Mali. REUTERS/Joe Penney
Talla

Sanarwar da babban hafsan sojin Mali ya fitar da yammacin ranar Talata, ta ce dakarun kasar sun kaddamar da farmaki ne a yankunan Timbuktu, Segou, Mopti da Bandiagara, tare da taimakon dakarun musamman na Turai, inda kuma suka samu nasara kan ‘yan ta’addan, da suka jagoranci tada kayar baya da aka kwashe shekaru goma ana fama da shi a Mali.

Sansanoni akalla 15 aka tarwatsa tare da kame mutane 8, da babura 35, aka kuma lalata wasu 15, sannan an kwace wayoyin hannu 37, kamar yadda sanarwar babban hafsan sojin kasar ta Mali ta tabbatar.

Ranar Asabar da ta gabata rundunar sojin Mali ta ce an kashe mata sojoji 8, yayin da su kuma suka kashe ‘yan tawaye 57, yayin gurmurzun da suka yi a yankin Arham da ke arewacin kasar, kusa da kan iyaka da Burkina Faso da Nijar mai fama da rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.