Isa ga babban shafi
Uganda

Uganda na shirin fara cin tarar wadanda suka ki karbar rigakafin Korona

Uganda na shirin kafa dokar fara cin tarar mutanen da suka ki yin allurar rigakafin cutar Korona, zalika za a iza keyar duk wanda kuma ya ki biyan tarar zuwa gidan Yari.

Wata ma'aikaciyar dauke da allurar rigakafin cutar Korona ta kamfanin AstraZeneca a asibitin Mulago da ke birnin Kampala, a ranar farko da aka kaddamar da shirin yi wa mutane rigakafin annobar a ranar 10 ga Maris, 2021.
Wata ma'aikaciyar dauke da allurar rigakafin cutar Korona ta kamfanin AstraZeneca a asibitin Mulago da ke birnin Kampala, a ranar farko da aka kaddamar da shirin yi wa mutane rigakafin annobar a ranar 10 ga Maris, 2021. AFP - BADRU KATUMBA
Talla

Za a kafa sabuwar dokar ce a karkashin wani gyara na dokar kiwon lafiyar jama'a, wadda majalisar dokokin kasar ta Uganda ke nazari a kai.

Ministar lafiya Jane Ruth Aceng ta shaidawa ‘yan majalisar a ranar Litinin cewa gyaran yana da mahimmanci don kare lafiya da rayukan mutane.

Sabuwar dokar ta ba da shawarar cin tarar shilling na Uganda miliyan 4, kwatankwacin dalar Amurka dubu 1,139 ga wadanda suka ki yin allurar rigakafi, duk wanda kuma ya ki biyan tarar, za a daure shi tsawon watanni 6 a gidan Yari.

Kawo yanzu kusan shekara 1 kenan da gwamnatin Uganda ta fara ba da allurar rigakafin Korona, sai dai  kusan mutane miliyan 16 kawai suka karbi rigakafin, daga cikin jumillar miliyan 45 da suka kasance yawan al’ummar kasar, matsalar da wasu jami’ai ke dangantawa da rashin yadda da sahihancin maganin a tsakanin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.