Isa ga babban shafi
Afirka - Rasha

AU ta yi Allah wadai da yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine

Kungiyar kasashen Afirka ta AU tayi Allah wadai da matakan da Rasha ta dauka na mamaye kasar Ukraine, inda ta bukaci gaggauta tsagaita wuta saboda yadda rikicin ke iya fadada zuwa babban yaki.

Hedikwatar kungiyar kasashen nahiyar Afirka da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Hedikwatar kungiyar kasashen nahiyar Afirka da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. RFI / Anne-Marie Bissada
Talla

Shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Senegal Macky Sall tare da shugaban gudanarwa Moussa Faki Mahamat sun bayyana matukar damuwa akan abinda ke faruwa a Ukraine a sanarwar hadin gwuiwa da suka gabatar.

Shugabannin sun bukaci Rasha da ta mutunta dokokin duniya tare da ‘yancin kasar Ukraine da iyakokin ta.

Sanarwar tace an bin tafarkin diflomasiya ne wajen warware rikici tsakanin kasashe biyu a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya maimakon tashin hankali.

Rahotanni sun ce akalla mutane 68 suka mutu a Ukraine tun bayan kaddamar da yakin da Rasha tayi cikin su harda soji da fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.