Isa ga babban shafi
Amurka - Rasha

Amurka ta laftawa Rasha takunkumai saboda kutsawa gabashin Ukraine

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da laftawa Rasha takunkumai, yana mai kiran amincewar da Rashan ta yi da ‘yancin yankuna biyu masu ballewa daga gabashin Ukraine a matsayin farkon mamayar da Rasha ta yi wa makwabciyarta, matakin da itama majalisar dinkin duniya ta bayyana a matsayin karya dokokin kasa da kasa.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

A wani takaitaccen jawabi da ya yi a ranar Talata, Biden ya yi turr da matakin da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ya dauka na amincewa da 'yancin kan Luhansk da Donetsk da kuma ba da izinin tura sojojin Rasha don wanzar da zaman lafiya a yankunan.

Shugaban na Amurka ya kuma kara da cewar idan har Rasha ta kara daukar wasu matakan na cigaba da mamayar Ukraine, ba zai bata lokaci ba, wajen sake kakaba mata wasu karin takunkuman, baya ga na jiya Talata da suka hada da yanke duk wata alakar hada-hadar kudi tsakanin gwamnatin Rasha kasashen yammacin Turai, da kuma hana ta shiga kasuwanninsu, sai kuma manyan cibiyoyin hada-hadar kudin Rashan biyu da takunkuman suka shafa, ciki har da bankin sojan kasar.

Ranar litinin, shugaba Putin ya amince da ‘yancin  Jamhuriyar Donetsk  da ta Luhansk (LPR) - yankunan da ake gwabza fada tsakanin 'yan aware masu samun goyon bayan Moscow da kuma gwamnatin Ukraine tun shekara ta 2014.

Daga nan ne Moscow ta rattaba hannu kan yarjeniyoyi da yankunan da za su ba ta damar tura sojojinta zuwa gabashin Ukraine.

Tuni dai sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi watsi da matakin Rasha na amincewa da ‘yancin yankunan biyu na ‘yan aware a gabashin Ukraine, wanda ya ce ya keta hurumin ‘yancin kan kasar, tare da kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.