Isa ga babban shafi
Oxfam-Tafkin Chadi

Mutane miliyan 38 za su fuskanci tsananin yunwa a yammacin Afrika- rahoto

Wani rahoto da hadakar kungiyoyin agaji 11 karkashi jagorancin Oxfam, ya yi gargadi kan yadda tsananin yunwa ke tunkarar karin mutum miliyan 11 a nahiyar Afirka cikin watanni 3 masu zuwa, alkaluman da ke matsayin kari kan mutane miliyan 27 da tuni suka fara fuskantar wannan matsala, wanda ke matsayin yunwa mafi tsanani da Afrika za ta gani a shekaru 10 da suka gabata.

Tuni dama matsalar ta tsananin yunwa ya kassara gabashin Afrika.
Tuni dama matsalar ta tsananin yunwa ya kassara gabashin Afrika. Oxfam East Africa
Talla

Rahoton wanda ke zuwa gabanin wani taron gamayyar kungiyoyin abinci na Turai da yammacin Afrika da kuma Sahel da zau tattauna matsalar karancin abinci a nahiyar, ya bayyana cewa matsalar yunwar zai kai kololuwa nan da watan Yuni matukar ba a dauki matakan da suka dace wajen yaki da karancin abinci ba.

Rahoton bisa jagorancin Oxfam ya ce wannan zai zama mafi munin lokacin da Afrika za ta fuskanci yunwa da jumullar mutum miliyan 38 wanda ke da nasaba da ibtila'in ambaliyar ruwa da karancin saukar ruwan sama baya ga lalacewar shuka da kuma uwa uba annobar corona da ta yi illa ga sassa daban-daban ciki har da kassara tattalin arzikin wadannan kasashe.

A cewar rahoton kungiyoyin agajin bisa jagorancin Oxfam kasashen da wannan matsala ta fi shafa sun hada da Burkina Faso da Nijar da Chadi da Mali da kuma Najeriya kasashen da ke cikin matsalar abinci tun sherkarar 2015.

Wata sanarwar kungiyar agaji ta Oxfam mai dauke da sa hannun daraktar shiyya mai kula da yammaci da tsakiyar Afrika Assalama Dawalack Sidi, ta ce tuni matsalar ta tilastawa miliyoyin mutane yin kaura daga muhallansu don samun saukin rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.