Kasar Somalia na gab da fadawa cikin halin yunwa
Hukumar agaji a Somalia ta ce kasar na gab da fadawa cikin halin matsananciyar yunwa sakamakon yadda mutanen da yawan su ya kai miliyan 4 da rabi yanzu haka ke cikin tsananin bukatar agajin abinci.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta ce wannan ne fari mafi muni da kasar za ta gani cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, dai dai lokacin da gonaki ke bushewa, farashin kayakin abinci da na ruwa kuma ke ci gaba da tashin gwauron zabi.
Wasu alkaluman Majalisar dinkin Duniya sun ce zuwa yanzu fiye da mutum dubu 700 ne suka tserewa matsugunansu tare da hijira zuwa wasu yankuna don samun abinci da ruwan sha.Rikicin siyasa na ci gaba da zazzafa a kasar inda kusan kasashe 30 ne a duniya suka bukaci ganin an cimma sulhu tsakanin yan siyasa a kasar ta Somalia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu