Isa ga babban shafi
Somalia

Dan kunar bakin wake ya kaiwa jami'an zaben Somalia hari

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan wata karamar motar bas mai cike da wakilai masu kula da zaben 'yan majalisar dokokin Somalia, inda ya kashe akalla mutane shida a birnin Mogadishu.

Jami'an tsaron Somalia tsare da hanyar da ta kai wajen da wani abu ya fashe a wani shingen binciken ababan hawa da ke kusa da fadar shugaban kasa a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, ranar 10 ga watan Fabrairu, 2022.
Jami'an tsaron Somalia tsare da hanyar da ta kai wajen da wani abu ya fashe a wani shingen binciken ababan hawa da ke kusa da fadar shugaban kasa a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, ranar 10 ga watan Fabrairu, 2022. © REUTERS/Feisal Omar
Talla

An kai harin kunar bakin waken ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a lokacin da motar bas din ke wucewa ta wata mahadar jama'a a kan hanyar da ta nufi ofishin shugaban kasar Somalia.

Abdikadir Abdirahman, darektan hukumar bada agajin gaggawa a Somalia, ya tabbatar da mutuwar mutane 6 a harin, sai dai kawo yanzu ba a bayyana sunayen mamatan ba.

Sai dai Saado Abdillahi, wani wakilin zabe da ke cikin motar bas din ya ce babu wanda ya ji rauni a cikinsu.

Abdillahi ya kara da cewar suna tsaka da tafiya cikin motar bas din suka ga wani ya ruga kansu amma ‘yan sanda suka bude masa wuta daga bisani damarar bam din dake jikinsa kuma ta tarwatse.

Tuni dai kungiyar al-Shabaab mai alaka da Al Qaeda, ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce ta kashe wakilai shida da jami'an 'yan sanda biyar.

An fara zaben 'yan majalisar dokokin Somalia a ranar 1 ga watan Nuwamba kuma da farko ya kamata a kawo karshensa a ranar 24 ga watan Disamba, amma a halin yanzu ana sa ran kammala shi a ranar 25 ga watan Fabrairu. Harin kuma da aka kai kan wakilan zaben na iya haifar da wani karin kalubale ga aiwatar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.