Isa ga babban shafi
Somalia

An sake kai mummunan harin bam a Somalia

Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a kan hanyar zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na Mogadishu babban birnin kasar Somalia, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla takwas, kamar yadda shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na birnin ya sanar.

Fararen hula a wurin da bama-bamai suka fashe a gundumar Hamarweyne da ke Mogadishu, Somalia, 12 ga Janairu, 2022.
Fararen hula a wurin da bama-bamai suka fashe a gundumar Hamarweyne da ke Mogadishu, Somalia, 12 ga Janairu, 2022. © REUTERS/Feisal Omar
Talla

Wani mazaunin Mogadishu Mohamed Osman ya ce girgizar da fashewar bama-baman ta haifar a ranar Laraba, sai da ta tuge bango da kuma rufin wani masallaci dake kusa da wajen, inda yake Sallah.

Ousman ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, lokacin da ya fito daga masallacin, ya ga gidaje da dama da suka ruguje, tare da sassan jikin mutanen da harin bama-baman ya rutsa da suu warwatse akan titi.

Kawo yanzu dai ba a bayyana wanda ke da alhakin tayar da bama-baman ba, zalika babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai farmakin.

A baya dai kungiyar al-Shabaab mai alaka da al-Qaeda ta sha daukar alhakin kai makamantan hare-haren, da kuma was una dabam kan dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.