Isa ga babban shafi
Somalia

Rikicin siyasar Somalia na barazanar kazancewa

Kasashen Turai da kuma wadanda ke makwaftaka da Somalia, sun bayyana fargaba kan takaddamar da ke ta’azzara tsakanin shugaban kasar da kuma Firaminista, inda a yanzu haka jami’an tsaro masu biyayya ga bangarorin da basa ga maciji, ke yin sintiri dauke da muggan makamai a wasu sassan birnin Mogadishu.

Sojojin Somalia masu biyayya ga Fitaminista Mohamed Hussein Roble yayin sintiri a wani sashin birnin Mogadishu, Somalia, 27 ga Disamban shekarar 2021.
Sojojin Somalia masu biyayya ga Fitaminista Mohamed Hussein Roble yayin sintiri a wani sashin birnin Mogadishu, Somalia, 27 ga Disamban shekarar 2021. REUTERS - FEISAL OMAR
Talla

Duk da cewa kawo yanzu ba a samu wata arrangama ba, fargaba a Mogadishu babban birnin Somalia na cigaba da karuwa, kan yiwuwar rikidewar takaddamar siyasar Shugaba Mohammed Abdulllahi Farmajo da Firaminista Hussein Roble zuwa kazamin rikici da muggan makamai.

A Talatar nan ce dai, sojojin da ke biyayya ga Firaminista Roble suka mamaye wasu wurare a kusa da fadar shugaban kasa, kwana guda bayan da shugaban ya sanar da dakatar da firaministan bisa zarginsa da cin hanci da rashawa, da kuma yin katsalandan a binciken da ake yi kan zarge zarge na kwace wasu filaye, yayin da shi kuma Firaministan ya zargi shugaban da yin zagon kasa ga zaben da ake shirin yi.

Firaministan kasar Somalia Mohamed Hussein Roble.
Firaministan kasar Somalia Mohamed Hussein Roble. Abdirahman Yusuf AFP/Archivos

Tuni dai masu sa ido na kasa da kasa suka bukaci bangarorin biyu da su sasanta rikicin nasu da ke ci gaba da tabarbarewa yayin da wasu dattijan siyasa da shugabannin gargajiya suka fara kokarin shiga Tsakani.

A gefe guda kuwa, gamayyar 'yan takarar shugabancin kasar ta Somalia ya bukaci shugaba Mohammed Farmaajo da ya gaggauta ficewa daga ofishinsa tare da yin kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa akan tuhumar da ake masa kan yiwa Firaminista juyin mulki da kuma gurfanar da wadanda suka taimaka masa.

Shugaban kasar Somalia, Mohamed Abdullahi Mohamed Farmajo.
Shugaban kasar Somalia, Mohamed Abdullahi Mohamed Farmajo. - AFP/Archivos

Daga ketare kuwa ofishin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afirka ya yi gargadi cewa Washington ta shirya daukar mataki kan wadanda ke kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya a Somalia.

Dangantaka tsakanin shugabannin kasar ta Somalia ta dade yin tsami, sai dai rikicin na baya bayan nan yafi tayar da hankula a ciki da wajen kasar, ganin yadda lamurra suka rincabe a daidai lokacin da hukumomin Somalian ke shirin gudanar da zabuka da kuma yaki da mayakan kungiyar Al Shebaab.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.