Isa ga babban shafi
Somalia

Mohamed Farmajo na Somalia ya sauke Firaministansa saboda rashawa

Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo, ya dakatar da firaministan kasar Mohamed Hussein Roble daga mukaminsa a cikin daren jiya bisa zargin rashawa, matakin da ke zuwa kwana guda bayan samun sabanin ra'ayi tsakanin shugagabannin biyu game da zaben kasar da aka jima ana dako.

Shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo, da Firaminista Mohamed Hussein Roble.
Shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo, da Firaminista Mohamed Hussein Roble. © Caasimada Online
Talla

Kwanaki kadan kafin sanarwar dakatar da shi da aka fitar cikin daren jiya, an zargin firaministan da kuma ministan tsaron cikin gida da karkata wasu filaye mallakin gwamnati, to amma duk da cewa an dakatar da firaministan, ministocinsa za su gaba da rike mukamansu.

Alaka tsakanin Firaminista Roble da shugaba Farmajo ta samu nakasu ne tsawon lokaci ko da ya ke batutuwa masu alaka da zaben kasar a baya-bayan nan shi ya sake tunzura batun.

Haka zalika ko a yau litinin Roble bai mayar da martini kan saukewar da shugaban ya yi masa, bai kuma ce uffan gan zargin rashawar da ake masa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.