Rikici tsakanin jami'an tsaro a Somalia ya raba daruruwan iyalai da gidajensu
Kazamin rikici tsakanin bangarori biyu na jami'an tsaro da ke gaba da juna a birnin Bosaaso mai tashar jiragen ruwa a Somalia, ya tilastawa daruruwan iyalai barin gidajensu.
Wallafawa ranar:
Jami’ai sun ce an kwashe kwanaki ana gwabza kazamin fada a birnin na Bosaaso, hedkwatar kasuwancin jihar Puntland mai cin gashin kanta a arewa maso gabashin kasar ta Somalia.
Wani jami'in yankin, Abdirizak Mohammed ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, har yanzu ba a san takamaiman adadin mutanen da suka rasa muhallansu ba a garin da ke gabar tekun Bahar Rum, amma tabbas yawansu ya kai daruruwa.
A ranar Alhamis din da ta gabata hukumar kula da jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce ta damu matuka game da karuwar tashe-tashen hankula a birnin na Bosaaso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu