Isa ga babban shafi

Kakakin gwamnatin Somalia ya tsallake rijiya da baya

A Somalia, kakakin  gwamnatin kasar Mohammed Ibrahim Moalimuu ya samu rauni biyo bayan wani harin kunar bakin wake da yan kungiyar Al Shebab suka kaiwa tawagar motar dake dauke da shi a babban birnin kasar Mogadiscio.

Harin yan kungiyar Al Shebab a kasar Somalia
Harin yan kungiyar Al Shebab a kasar Somalia - AFP
Talla

Fadar Firaministan kasar ce ta sanar da harin da aka kaiwa ayarin tawagar kakakin gwamnatin,da aka bayyana cewa ya samu rauni duk da cewa mutumen da ya kai harin ya yi kokarin ya makalewa motar da jami’in gwamnatin kasar ta Somalia ke ciki ka fi daga bisali ya tayar da bam dake jinkin na sa.

Wani harin kunar bakin wake a birnin Mogadiscio
Wani harin kunar bakin wake a birnin Mogadiscio © AFP - STRINGER

Yan kungiyar Al Shebab sun dau alhakin wannan harin da aka kaiwa kakakin gwamnatin kasar ta Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.