Isa ga babban shafi
Somalia

Amurka ta kakabawa jami'an Somalia takunkumi kan jinkirta zabe

Gwamnatin Amurka ta sanar da haramtawa jami'ai da wasu daidaikun ‘yan Somaliya takardar izinin shiga kasar, inda ta zarge su da raguza tsarin dimokuradiyya kasar tasu.

Shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo, da Firaminista Mohamed Hussein Roble.
Shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo, da Firaminista Mohamed Hussein Roble. © Caasimada Online
Talla

Matakin na Amurka ya zo ne sa'o'i kadan bayan da shugabannin Somalia suka tsawaita zaben 'yan majalisar zuwa ranar 15 ga watan Maris bayan gaza kammala zaben a ranar 25 ga Fabrairu.

Zaben wanda aka fara a watan Nuwamban da ya gabata, ya kamata a gudanar da shi ne shekara guda da ta wuce amma aka dakatar da shi sakamakon jinkiri da aka samu da suka hada da rashin cimma matsaya kan yadda za a gudanar da zaben, da kuma rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da firaminista a Somalian.

Ya zuwa yanzu dai, an zabi 179 daga cikin 275 na ‘yan majalisar a Somalia. Kuma ‘yan majalisar ne za su zabi shugaban kasa, amma har yanzu ba a sanya ranar da za a gudanar da zaben na shugaba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.