Isa ga babban shafi

Daurin rai da rai ya hau kan Compaore saboda kashe Thomas Sankara

Wata kotun soji a Burkina Faso ta yanke wa tsohon shugaban kasar Blaise Compaore hukuncin daurin rai-da-rai bisa samunsa da laifin kisan tsohon shugaban juyin juye halin kasar Thomas Sankara a shekarar 1987.

Tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaore
Tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaore REUTERS/Noor Khamis
Talla

Mutanen da ke zaune a cikin kotun sun kaure da tafi a yayi da suke sauraron hukuncin da alkalin ya shafe lokaci mai tsawo yana karantawa, lamarin da ke kawo karshen shari’ar da ta janyo cece kuce a kasar tsawon shekaru 34.

Kotun ta kuma yanke wa Hyacinthe Kafando, hafsan sojin da ya jagoranci gungun sojojjin da suka kashe Sankara hukuncin daurin rai-da-rai, tare da Gilbert Diendere, wani kwamandan soji mai ci alokacin kisan gillar da ya zo daidai da lokacin juyin mulkin da ya dora. Campaore bisa karagar mulki.

Campaore, wanda ya yi zaman hijira a kasar Ivory Coast bayan da aka zanga zangar da al’ummar kasar suka gudanar ta kifar da  gwamnatinsa a shekarar 2014 da Kafando wanda yake hijira tun a shekarar 2016 ba sa nan aka yi musu hukunci.

Dimbim mutane ne suka yi bibiyar wannan shari’ar da aka shafe watanni 6 ana yi a wannan kasa da ke yankin Sahel, wanda kisan Sankara ya ci gaba da kasancewa wani al’amari mara dadin ji a tarihinta.

Sankara, wanda ya yi riko da akidar Markasanci, kuma yake caccakar kasashen yamma, ya gamu da ajalinsa ne a ranar 15 ga watan Oktoban 1987 yana matsayin kaftin din soji mai shekaru 33 sakamakon harbin sa da aka yi da bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.