Al'ummar Gambia na zaben 'yan majalisar dokoki
Al'ummar Gambia na kada kuri'ar zaben 'yan majalisar dokokin kasar a wannan Asabar, zaben da wasu ke ganin ka iya karfafawa shugaba Adama Barrow ikonsa bayan da ya sake lashe zabe a shekarar bara.
Wallafawa ranar:
‘Yan takarar shiga zauren majalisar dokokinkasar ta Gambia dai za su fafata ne akan kujeru 58 kan wa'adin shekaru biyar.
Sai dai daga cikin kujerun ‘yan Gambia za su zabi 53 uku ne, yayin da shugaba Barrow zai bayyana sunayen ragowar biyar da zai zaba, cikinsu har da shugaban majalisar.
Za a bude rumfunan zabe da karfe 8:00 na safe sannan a rufe da karfe 5 na yamma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu