Isa ga babban shafi

Faransa ta bayyana shakku kan ikirarin Mali na kashe 'yan ta'adda a Moura

Manyan kasashen duniya sun fara mayar da martani kan nasarar kashe daruruwan ‘yan ta’adda da sojojin Mali ke ikirarin samu nasarar  yi a yankin Moura, inda a ranar Juma’a tsohuwar uwargijiyar Mali wato Faransa ta bayyana shakku kan gaskiyar wannan ikirarin.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian. © AFP/Alik Keplicz
Talla

Cikin wata sanarwa ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya bayyana shakkunsa, bisa dogari da bayanan wasu shaidu da ke cewa daruruwan mayakan da gwamnatin sojin Mali ke ikirarin kashewa fararen hula ne, ba ‘yan ta’adda ba.

Le Drian ya kuma bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya domin gano gaskiyar al’amarin da ya faru a yankin Moura.

Sai dai a yayin da Faransa ta bayyana na ta matsayin, Rasha kuwa jinjinawa dakarun kasar Mali ta yi bisa nasarorin da suke samu kan ‘yan ta’adda, bayan kashe mayakan masu ikirarin Jihadi fiye da 200 da suka yi cikin ‘yan kwanaki a yankin Moura, nasarar da Rasha ta bayyana a matsayin gagaruma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.