Dakarun MNJTF sun halaka mayakan ISWAP 18 a Tafkin Chadi
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa sun kashe wasu mayaka 18 da ake kyautata zaton na kungiyar ISWAP ne a yankin tafkin Chadi.
Wallafawa ranar:
Rundunar da a takaice ake kira da MNJTF ta kunshi sojoji daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru.
Bayanai sun ce dakarun hadin gwiwar sun halaka ‘yan ta’addan ne tun a ranar 3 ga watan nan na Afrilu bayan hare-haren da suka kaddamar kansu tsawon mako guda a yankuna da dama cikinsu har da Malam Fatori, Gashigar, da kumaTalata Ngam.
Baya ga kashe mayakan na ISWAP, sojojin sun lalata manyan bindigogi tare da kwato makamai da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu