Isa ga babban shafi

Sauyin yanayi zai iya fadada aukuwar guguwa a sassan Afirka - Kwararru

Wani sabon rahoto da hukumar da ke kula da sauyin yanayi ta duniya ta fitar ya nuna yadda kasashen kudu maso gabashin Afrika ke ci gaba da fuskantar annobar mahaukaciyar guguwa da ambaliyar ruwa duk a dalilin sauyin yanayin da duniya ke fuskanta.

Mutane tsaye a gefen wata hanyar da guguwa mai dauke da mabliyar ruwa ta lalata a Malawi. 26 ga Janairu, 2022.
Mutane tsaye a gefen wata hanyar da guguwa mai dauke da mabliyar ruwa ta lalata a Malawi. 26 ga Janairu, 2022. GERALD NTHALA via REUTERS - GERALD NTHALA
Talla

Rahoton ya ce kasashen Madagascar da Malawi da Mozambique ne suka fi fukantar iftila’in mahaukaciyar guguwar a yankin kudu maso gabashin Afrikan.

Cikin mako 6 kadai wannan yanki ya ci karo da ambaliyar ruwa mai muni har sau uku da kuma mahaukaciyar guguwa sau biyu, kuma dukannin su sun tafi da rayuka da dukiyoyin jama’a.

A cewar rahoton fiye da mutane miliyan guda wannan tashin hankali ya shafa yayin da sama da dari 230 suka rasa rayukansu.

Rahoton hukumar ya kuma ci gaba da cewa yankin ya ci karo da wannan tashin hankali ne dalilin sauyin yanayi da duniya ke fama da shi, abinda ya sanya ruwan sama kamar da baki kwarya baya daukewa yayin da yake haddasa ambaliyar ruwa.

Hukumar ta cikin rahoton ta jadadda cewa dukkan alamu na nuna cewa za’a ci gaba da samun wannan tashin hankali a yankin, yayin da zai ci gaba da fadada zuwa sauran sassan nahiyar ta Afrika, matukar ba a dauki matakin da ya dace cikin hanzari ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.