Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

Burkina Faso zata dauki sabbin sojoji dubu 3 don yaki da ta'addanci

Gwamnatin Burkina Faso zata dauki karin sojoji dubu uku domin kara karfin sojojin kasar dake fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi, da akasari ke kaiwa ga rasa rayukan sojoji da fararen hula.

Shugaban rikon kwaryar mulkin sojin Burkina Faso, Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba yayin sanya hanu kan wa'adin da zasu yi kafin zabe.
Shugaban rikon kwaryar mulkin sojin Burkina Faso, Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba yayin sanya hanu kan wa'adin da zasu yi kafin zabe. AFP - LEONARD BAZIE
Talla

Ministan Tsaron kasar, Janar Aimé Barthélémy Simporé yace, da farko an shirya daukar sojoji dubu biyu ne daga ranar  1 ga watan Yuni, da kuma Karin hafsoshi na musamman guda dubu daya, amma shirin zai soma daga ranakun 4 – 31 ga watan Mayu.

Kuma za’a zakulo zaratan ne daga jihohin kasar 13.

An yi kiyasanin Burkina Faso na da sojojin tsakanin dubu 15 zuwa 20, kuma akasarinsu sojojin kasa ne, da suka shafe shekaru bakwai suna fafatawa da mayaka masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.