Isa ga babban shafi

Sojojin Mali sun sake kashe 'yan ta'adda a yankin tsakiyar kasar

Rundunar sojin Mali ta ce dakarunta sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 12, cikinsu har da wani mai takardun shaidar zama bafaranshe kuma dan kasar Tunisia, yayin hare-hare ta sama da ta kai a yankin tsakiyar kasar.

Wasu sojojin kasar Mali.
Wasu sojojin kasar Mali. © Serge Daniel/RFI
Talla

Sau biyu ne dai sojojin na Mali suka kai hare-hare a cikin dajin Ganguel mai tazarar kilomita 10 daga garin Moura tun daga ranar Alhamis da ta gabata.

Rundunar sojin ta Mali ta ce ta kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri game da wani gungun ‘yan ta’addan da suka yi tattaki domin karfafa takwarorinsu na kungiyar GSIM a garin na Moura, inda a makon jiya dakarun kasar ta Mali sukasanar da kashe ‘yan ta’adda 203.

Kasashen Turai da suka hada da Faransa da Jamus na bayyana shakku kan sahihancin rahoton kashe ‘yan ta’addan da sojojin Mali suka yi a garin Moura, inda a makon da ya gabata, ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.