Yan adawar Chadi na zargin Gwamnati da kafar ungulu
Yan tawagar Chadi sun zargi gwamnatin kasar da jinkirin da ake samu wajen kulla yarjejeniya a taron zaman lafiya dake gudana a Doha.
Wallafawa ranar:
Wannan taron na tattauna wa da ke gudana a Doha babban birnin Qatar an shirya shi ne ga kungiyoyi kusan 50 dake dauke da makamai a kasar Chadi, wanda aka shirya gudanar wa tun a ranar 27 ga watan fabarairu, aka kuma daga shi zuwa watan maris.
Tattaunawar da za’a warware matsalolin kasar da aka shirya yi a ranar 10 ga watan Mayu zata kunshi 'yan adawar siyasa da wadanda ke rike da makamai, sannan a taron ne ya kamata a shirya managarcin tsari da za a samar da ingantaccen kundin tsarin mulkin kasar da kuma tsara sahihin zabe mai cike da adalci.
Kakakin gwamnatin Abderaman Koulamallah ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, zarge-zarge ne ake musu da bai dace ba, domin suna da sha'awar ganin an kawo karshen tattaunawar da suka shirya a Qatar kafin ranar 10 ga watan Mayu domin 'yan siyasa da sojoji su kasance cikin tattaunawar da za a gudanar cikin adalci.
Indai ba a mance ba an dai nada Mahamat Idriss Deby Itno ne a matsayin shugaban majalisar soji ta rikon kwarya (CMT) da ta kunshi janar-janar 15, bayan sanarwar mutuwar mahaifinsa, Marshal Idriss Deby, a ranar 20 ga watan Afrilun shekara ta 2021, da aka kashe yayin fafatawa da yan tashin tashina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu