Sweden ta tasa keyar wani dan Rwanda domin amsa tuhuma kan kisan kare dangi
Hukumomin Kasar Sweden sun tasa keyar wani dan kasar Rwanda zuwa gida domin amsa tuhuma dangane da zargin da ake masa na hannu a kisan kare dangin da aka yi a kasar.
Wallafawa ranar:
Masu gabatar da kara a Kigali sun ce an mika musu Jean Paul Micomyiza yau laraba, yayin da suka godewa hukumomin Sweden akan taimaka musu da suka yi wajen yaki da kama karya.
An kama Micomyiza mai shekaru 50 a Sweden ne a watan Nuwambar shekarar 2020 sakamakon sammacin haka da Rwanda ta gabatar, yayin da akayi ta shari’a akan halarcin tasa keyar sa gida domin fuskantar tuhumar ko kuma akasin haka.
Ana tuhumar sa ne da hannu wajen neman Yan kabilar Tutsi inda suke nuna su domin hallaka su a shekarar 1994 lokacin yana matashi mai shekaru 22.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu