Isa ga babban shafi

Macky Sall na son a kafa hukumar tantance tattalin arziki mallakin Afirka

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya yi kira da a samar da hukumar tantance makoma da kuma karfin tattalin arzikin kasashen Afirka mallakin nahiyar, yana mai cewa, tsarin tantancewar da hukumomin kasa da kasa ke amfani da shi, ya sanya kasashen Afirka fuskantar wahalhalu da kuma tsadar neman basussuka.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall.
Shugaban kasar Senegal Macky Sall. AP - John Thys
Talla

Sall, wanda a halin yanzu shi ne shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, ya bayyana haka ne, yayin wata hira da gidan rediyo mai zaman kansa na RFM da ke kasar mai hedikwata a Faransa, a yau Lahadi.

Kalaman shugaban na Senegal sun zo ne a jajibirin babban taron tattalin arzikin da za a yi a Dakar na shekarar 2022, wanda masana tattalin arzikin Afirka suka shirya.

A cewar shugaba Sall, a cikin shekarar 2020, lokacin da duk tattalin arzikin duniya ke fama da tabarbarewar annobar Covid-19, 18 daga cikin 32 na kasashen Afirka da akalla daya daga cikin hukumomin lamunin kasa da kasa ya tantance tattalin arzikin su, sun fuskanci raguwar kimar da suke da ita.

Hakan na nufin kashi 56 cikin 100 na kasashen Afirka sun samu raguwar kimar da suke da ita, dangane da samun karbar basussuka, idan aka kwatanta da kashi 31 na kasashen duniya a daidai wannan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.