Isa ga babban shafi
Mali-G5 Sahel

Mali ta fita daga kawancen G5 Sahel mai yaki da ta'addanci

Gwamnatin mulkin sojin Mali ta sanar da janyewar kasar daga gungun kasashe biyar masu yaki da ayyukan ta’addanci da ake kira G5-Sahel, tare da bayyana kungiyar a matsayin wadda ake juyawa daga waje.

Assimi Goita, shugaban gwamnatin soji Mali.
Assimi Goita, shugaban gwamnatin soji Mali. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

A cikin daren jiyan ne gwamnatin mulkin sojin Mali ta sanar da janyewar daga wannan gungu da ya hada Burkina Faso, Chadi, Mauritania da kuma jamhuriyar Nijar, tare da kawo karshen duk wata alakar aikin soji ko yaki da ayyukan ta’addanci karkashin inuwar wannan kungiya da aka kaddamar tun 2014.

Sanarwar ta yi zargin cewa akwai wata kasa wadda ba mamba ba ce a gungun na G5-Sahel amma kuma take haddasa tarnaki wajen ganin cewa ba ta gudanar da taron kungiyar da aka tsara yi ciikin watan Fabrairun da ya gabata a birnin Bamako ba, wanda a lokacinsa ne ya kamata a danka ragamar shugabancin kungiyar a hannun Mali.

Har ila yau sanarwar wadda ministan tsaron cikin gida kanar Abdoulaye Maiga ya sanya wa hannu ta ce, akwai wata kasa mamba a G5-Sahel da ke adawa da gudanar da taron a Mali saboda dalilai na siyasa.

To sai dai duk da cewa ba a ambaci sunan wata kasa ba a wannan sanarwa, alaka tsakanin Mali da kasashen Turai ciki har da Faransa ta yi tsami ne daga lokacin da aka ruwaito cewa sojin hayar Wagner na kasar Rasha sun shiga kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.