Isa ga babban shafi

An kama shugaban 'yan adawa a Chadi bayan zanga-zangar adawa da Faransa

An kama wani jigon kungiyar ‘Yan adawa a kasar Chadi bayan barkewar wata mummunar zanga-zangar kin jinin Faransa da ta sanya gwamnatin mulkin sojan kasar yin gargadi mai karfin gaske, kamar yadda Kungiyar sa tare da jami’an tsaro suka baiyana.

Waasu masu Zanga-zangar adawa da Faransa a kasar Chadi, bayan kiran gamayyar kungiyiyin adawa ta Wakit Tama, a Ndjamena, Chadi, 14 ga Mayu, 2022.
Waasu masu Zanga-zangar adawa da Faransa a kasar Chadi, bayan kiran gamayyar kungiyiyin adawa ta Wakit Tama, a Ndjamena, Chadi, 14 ga Mayu, 2022. © Madjiasra Nako/RFI
Talla

Andai kama jigon ‘yan adawar Max Loalngar ne wanda shine jami’in hada hancin gungun ‘yan adawa ta Wakit Tamma, sanadiyar aiwatar da wata mummunar zanga-zangar da ta juye ta zama tashin hankali, a cewar rundunar ‘yansanda  kamar yadda ta wallafa a shafin ta na sada zumunta wato facebook.

Mai Magana da yawun gungun “yan adawar Micheal Barka ya shaidawa AFP cewa, wasu mutane ne cikin wasu motoci guda biyu suka same shi  a wajen mahaifiyar shi suka kuma yi awun gaba da shi suka kai shi inda ba a iya tantance wa ba.

Kungiyar ta Wakit Tamma dai na daya daga cikin wadanda suka shirya zanga zangar ranar asabar wadda ke zargin kasar Faransa wacce ta yi wa Chadi mulkin mallaka da goyon bayan kafa mulkin soji a kasar ta Chadi.

Wakilin kamfanin dillancin labarun Faransa AFP ya baiyana cewar tabbas anyi wannan zanga zangar sannan an kona tutocin Faransa biyu kana aka kona gidajen mai mallakin kasar guda bakwai tare da jikkata gomman 'Yan sanda, acewar hukamar 'yan sandan Kasar ta Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.