Isa ga babban shafi
Sahel-Faransa

Macron zai gana da shugabannin yankin Sahel a Paris

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai gana da shugabannin kasashen yankin Sahel yau juma’a don tattaunawa kan barazanar tsaron da yankin ke fuskanta sakamakon tsanantar hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

Shugaba Emmanuel Macron yayin tarbar takwaransa na Mali Mahamat Idriss Deby, a fadar Elysee da ke birnin Paris yau juma'a 12 ga watan Nuwamban shekarar 2021.
Shugaba Emmanuel Macron yayin tarbar takwaransa na Mali Mahamat Idriss Deby, a fadar Elysee da ke birnin Paris yau juma'a 12 ga watan Nuwamban shekarar 2021. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Ganawar ta Macron da shugabannin na kassahen Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore da Mohamed Bazoum na Nijar baya ga Mahamat Idris Deby da ke rikon kwarya a Chadi wani bangare ne na babban taron kasashen duniya da ke gudana a Faransar wanda ya mayar da hankali kan zaman lafiyar Libya.

Tun a jiya Alhamis fadar Elysee ta sanar da shirin ganawar shugabannin a wani bangare na taron na yau, ganawar da ke zuwa dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin Mali da Faransar wadda ta yi mata mulkin mallaka musamman bayan juyin mulkin baya-bayan nan da Paris ta kalubalanta.

Babu dai cikakken bayani ko Firaminista Choguel Kokalla Maïga na Malin na cikin jerin shugabannin da Macron zai gana da su a taron na yau.

Alaka ta kara tsami tsakanin kasashen biyu bayan musayar zafafan kalamai musamman bayan da Paris ta fara janye dakarunta da ke taimakawa a yakar ta’addanci da kuma yunkurin Bamako na daukar Sojin hayan Wagner daga Rasha don taimaka mata fatattakar ayyukan ta’addanci.

Ganawar ta Macron da kassahen na Sahel 3 na zuwa a wani yanayi da ayyukan ta’addanci ke ci gaba da tsananta a ilahirin kasashen 3 inda ake rasa rayukan dakaru a kusan kowacce rana baya ga daruruwan fararen hula da hare-haren ta’addancin kan shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.