Isa ga babban shafi
RIKICIN-SAHEL

Yadda 'Yan ta'adda ke samun makamai a Yankin Sahel - Amnesty

Wani rahotan binciken da kungiyar Amnesty International ta gabatar, yace hotunan bindigogin da ‘Yan bindiga dadi da ‘Yan ta’adda ke amfani da su a Yankin Sahel na Afirka sun nuna cewar wadanda kamfanin Zastava dake kasar Serbia suka sarrafa ne.

Yan bindiga dadi a Najeriya
Yan bindiga dadi a Najeriya © Daily Trust
Talla

Kungiyar tace an gano makaman da kasar Serbia ke sarrafa su sakamakon hotunan bidiyo da aka yada a kafofin sada zumunta wanda ke nuna ‘Yan tawaye da ‘Yan ta’adda a yankin Sahel na dauke su tare da mayakan ISIS da suka dauki alhakin hallaka daruruwan fararen hula.

Rahotan ya bayyana cewar makaman na daga cikin wadanda aka sarrafa su a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kuma suna daga cikin sabbi kamar yadda takardun cinikin su tsakanin Serbia da gwamnatin Bukina Faso suka nuna, abinda ke nuna cewar an sayarwa gwamnatin kasar ne kafin fadawar su hannu ‘Yan ta’adda.

Sojin Guinea bayan juyin mulki 05/09/21.
Sojin Guinea bayan juyin mulki 05/09/21. AFP - CELLOU BINANI

Masana makamai daga kungiyar Amnesty International sun yi nazari akan irin wadannan rahotannin sama da 400 daga kasashen Burkina Faso da Mali, biyu daga cikin kasashen da suka yi dumu dumu cikin rikicin yankin Sahel, tare da wasu hotunan da aka tantance su da kuma faifan bidiyon da kungiyoyin ‘Yan ta’adda suka yada a kafofin sada zumunta tsakanin watan Janairun shekarar 2018 zuwa Mayun shekarar 2021.

Hotunan sun nuna makaman da mayakan ke dauke da su ciki harda na mayakan kungiyar IS dake yakin Sahara da Jama’at Nusrat al Islam da tayi mubayi’a ga kungiyar Al-Qaeda.

Kungiyar tace yayin da wasu daga cikin makaman kirar Kalshnikov ne da Tarayyar Soviet ke kerawa, an gano wasu nau’i 12 da mayakan ke dauke da su wadanda kamfanin Zastava dake kasar Serbia ne ya kera su.

Wasu makaman da aka karbe a hannun Yan bindiga a Afirka
Wasu makaman da aka karbe a hannun Yan bindiga a Afirka REUTERS/Sia Kambou/Pool

Makaman sun hada da bindiga kirar M02 Coyote mai sarrafa kan ta da bindigogi kirar M92 da M05 da kuma samfurin M05E3 wadanda aka samar kafin fara tashin hankalin arewacin Mali a shekarar 2011.

Amnesty tace babu tabbacin gano wadanda suka mallaki makaman, amma akwai alamun dake nuna cewar ko dai an karkata su ne wajen baiwa ‘Yan ta’adda ko kuma sun yi nasarar kwace su ne a filin daga.

Kasar Serbia ta sanya hannu a yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya dake haramta cinikin makamai ta bayan gida, wanda ya kunshi haramta safarar makaman idan ana fargabar cewar za ayi amfani da su wajen take hakkin Bil Adama.

Shugaban Hukumar kwastam Hameed Ali na gabatar da wasu makaman da aka kama a Lagos
Shugaban Hukumar kwastam Hameed Ali na gabatar da wasu makaman da aka kama a Lagos © Tell Magazine

Amnesty tace yarjejeniyar ta kunshi bukatar kasashe su yi nazari akan illar karkata makaman ga wasu bangarori bayan sayarwa gwamnatoci, musamman kanana da matsakaitan makaman da ake iya safarar su.

Tsakanin shekarar 2015 zuwa 2020 kasar Serbia ta shaidawa yarjejeniyar makaman cewar ta aike da bindigogi dubu 20,811 zuwa kasar Burkina Faso tare da manyan bindigogi 4,000 da kanana 600 da kuma masu sarrafa kan su 290.

Daraktan kasuwanci, tsaro da kare hakkin Bil Adama na kungiyar Amnesty, Patrick Wilcken yace a shekarar 2020 da Serbia ta turawa Burkina Faso makamai bayan fara rikici da kungiyoyin dake dauke da makamai a kasar, ya dace ace tayi hasashen cewar ana iya amfani da su wajen take hakkin Bil Adama.

Wilcken yace binciken su ya nuna cewar, makaman na Serbia na fuskantar barazana fadawa hannun ‘Yan ta’adda a yankin Sahel wadanda ke amfani da su wajen jefa yankin cikin tashin hankali.

Gwamnan Rivers na duba makaman da 'Yan bindiga suka mika a Fatakwal
Gwamnan Rivers na duba makaman da 'Yan bindiga suka mika a Fatakwal © The Sun

Kungiyar Amnesty ta kuma bayyana cewar kasashen Jamhuriyar Czech da Faransa da kuma Slovenia na daga cikin wadanda suka tura kanana da matsakaitan makamai ga gwamnatocin dake Yankin Sahel tun bayan barkewar rikici a yankin.

Hukumomin Serbia sun ki cewa komai dangane da rahotan binciken da kungiyar Amnesty International ta gudanar, yayin da kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar ke fuskantar illar amfani da wadannan makamai da ‘Yan ta’adda ke yi a cikin kasashen su.

A watan Nuwambar bara an gano harsasan da aka kera a Serbia da hukumomin Najeriya suka yi amfani da su wajen murkushe masu zanga zanga a birnin Lagos, yayin da aka gano makamai kiran kamfanin Krusik dake Serbia da aka yi amfani da su a rikicin Yankin Nagorno-Karabakh tsakanin kasashen Azerbaijan da Armenia.

Wasu daga cikin makaman da tubabbun Yan bindiga suka gabatar a Zamfara
Wasu daga cikin makaman da tubabbun Yan bindiga suka gabatar a Zamfara © Premium Times

A watan Yunin bara gwamnatin Libya tayi amfani da makaman Serbia wajen murkushe ‘Yan tawaye a Tripoli da kuma kwace iko da birnin.

A watan Oktobar shekarar 2019, hukumomin kasar Iraqi sun yi amfani da gurnetin da akayi da gas a Serbia wajen tarwatsa masu zanga zanga a Bagadaza, tare da gurneti kirar M99 da Yan Sanda ke amfani da shi maimakon hayaki mai sa hawaye.

Har ila yau an gano makamai da dama da Serbia ke sarrafawa a rikicin kasar Syria a shekarar 2016.

Yanzu haka irin wadannan makamai sun zama ruwan dare a hannun mutanen da doka bata baiwa damar mallakar su ba a kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Mali da Burkina Faso da Mali da Kamaru, abinda ya zafafa tashin hankali da zuba da jini a kasashen.

Wasu daga cikin 'Yan bindigar Najeriya sun bayyana cewar a cikin sauki suke samun wadannan makamai a ciki da wajen Najeriya, amma jami'an tsaro da na kwastam har ya zuwa wannan lokaci basu iya dakile safarar su zuwa cikin kasar ba.

Abin tambaya daga masana shine, ta yaya irin wadannan makamai ke fadawa hannun ‘Yan ta’adda ko ‘Yan bindiga dake amfani da su wajen kashe fararen hula ba tare da kaukautawa ba?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.