Isa ga babban shafi
FARANSA-SAHEL

Macron zai sake fasalin yaki da ta'addanci a Sahel

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana shirin janye dakarun kasar sa dake yaki da ‘Yan ta’adda a Yankin Sahel na kusan shekaru 10 a karkashin rundunar Barkhane da kuma bukatar kafa wata sabuwar runduna ta kasashen duniya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na gabatar da sabon shirin yaki da ta'addanci a Yankin Sahel
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na gabatar da sabon shirin yaki da ta'addanci a Yankin Sahel © AFP/Pascal Rossignol
Talla

Yayin jawabi ga manema labarai, shugaban yace za’a kawo karshen rundunar Barkhane, yayin da za’a kafa wata sabuwar runduna ta sojojin kasashen duniya da aka yiwa suna Takuba wadda zata kunshi daruruwan sojojin kasar.

Kasar Faransa yanzu haka nada dakaru 5,100 a Yankin Sahel wadanda ke yaki da Yan ta’adda kuma an baza su ne cikin kasashe da dama dake yankin.

Macron yace lokaci yayi da za’a sake fasalin rawar da dakarun Faransa ke takawa wajen sake tsarin zaman sojojin kasar a Yankin Sahel baki daya.

Shugaban yace nan gaba kadan za’ayi cikakken bayani kan yadda dakarun zasu kasance da kuma irin rawar da zasu taka baki daya.

Wani sojan Faransa na rundunar Barkhane yayin sintirin kakkabe 'yan ta'adda a garin Tin Hama dake kasar Mali, ranar 19 ga watan Oktoban 2017.
Wani sojan Faransa na rundunar Barkhane yayin sintirin kakkabe 'yan ta'adda a garin Tin Hama dake kasar Mali, ranar 19 ga watan Oktoban 2017. © REUTERS/Benoit Tessier/File Photo

An kafa rundunar Barkhane ne a watan Janairun shekarar 2013 lokacin da Faransa ta shirya kai dauki domin yaki da Yan ta’adda a yankin Sahel.

Sabuwar rundunar Takuba da za ta maye gurbin Barkhane, a halin yanzu ta kunshi dakaru 600 ne daga kasashen Turai, rabinsu Faransanwa ne, sai 140 daga Sweden, saura daga Estonia da kuma Jamhuriyar Czech.

An kwashe shekaru shugaban Faransa Emmanuel Macron na neman taimakon kawayen kasar dake Yammacin duniya domin daukar nauyin yakin dan ganin an karkade Yan ta’addan dake yiwa yankin Sahel illa.

Dakarun kasar Faransa take aikin yaki da ta'addanci a yankin Sahel yayin sintiri a garin Inaloglog dake Mali, cikin watan Oktoban 2017.
Dakarun kasar Faransa take aikin yaki da ta'addanci a yankin Sahel yayin sintiri a garin Inaloglog dake Mali, cikin watan Oktoban 2017. © REUTERS/Benoit Tessier/File Photo

Kisan da aka yiwa shugaban kasar Chadi Idris Deby wanda babban abokin tafiyar Faransa ne da kuma juyin mulkin da akayi a Mali sun dada haifar da barazanar lafiya a Yankin.

Wani bangare na jawabinsa, shugaba Macron ya ce matakin kungiyar Ecowas na amincewa da kanar Assimi Goita a matsayin shugaban Mali babban kuskure ne. 

Faransa dai ta tura sojoji zuwa Mali ne a watan janairun 2013, bayan da ‘yan ta’adda suka mamaye yankin arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.