Isa ga babban shafi
FARANSA - nIJAR

Faransa zata maida hankali Nijar wajen yaki da ta'addanci a Sahel

Ministan Tsaron Faransa Florence Paly ta ziyarci Nijar inda ta gana da shugaban kasa Bazoum Mohammed akan shirin kasar na sake fasalin yakin da take yi da ‘Yan ta’adda a yankin Sahel.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da ministar tsaron Faransa Florence Paly
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da ministar tsaron Faransa Florence Paly © Niger Presidency
Talla

Ita dai wannan ziyarar ta biyo bayan sanarwar da shugaban kasa Emmanuel Macron yayi na rage yawan dakarun Faransa dake yaki da Yan ta’adda a Yankin Sahel da kuma rufa wasu sansanonin da suke a Mali domin mayar da su Nijar.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da tawagar ministan tsaron Faransa Florence Paly
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da tawagar ministan tsaron Faransa Florence Paly © Niger Presidency

Ma’aikatar tsaron Faransa tace an dade da shirya wannan ziyarar domin tattauna yadda ake shirin baiwa Nijar wani sabon matsayi na yaki da Yan ta’addan da sojojin Faransa keyi a yankin Sahel.

A watan Yuni shugaban Faransa ya bayyana shirin rage sojojin kasar daga sama da 5,000 dake aiki a karkashin kungiyar Barkhane zuwa tsakanin 2,500 zuwa 3,000, kuma zasu mayar da hankali ne kawai wajen yaki da ta’addanci da kuam taimaka sojojin kasashen dake yankin.

Ma’aikatar tsaron Faransa tace tashar jiragen Faransa dake Nijar zai taka rawa wajen baiwa jiragen yakin kasar tashi suna kai hare hare a yankunan da Yan ta’adad suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.