Isa ga babban shafi

Rusau a unguwar Dikolo a Kamaru ya haifar da zanga-zanga

‘Yan sandan Kamaru sun baiwa wasu masu zangar a birnin Douala cibiyar kasuwancin kasar kariya, duk da cewa basu samu izinin gudanar da tattakin ba a hukumance.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Kamaru
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Kamaru © RFI/Amélie Tulet
Talla

Daruwan mutane ne suka gudanar da zanga- zangar kan abin da suka kira rashin adalci da aka nuna wa al’ummar anguwar Dikolo, da aka rusawa gidaje domin gina katafaren Otel a can.

Jama'a na ci gaba da kokawa ganin ko in kula da hukumomin ke nunawa,duk da cewa wasu bayyanai na nuni cewa hukumomin na nazari don samar da mafita cikin sauki.

Wasu masu zanga-zangar da suka fito daga wasu anguwannin na daban sun shaidawa manema labarai goyon bayansu ga mazauna Bali-Dikolo na marasa galihu da akayi korar wulakanci daga gidajensu raka saka, da nufin kawata birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.