Isa ga babban shafi

Ministocin Faransa 2 sun gana a Nijar gabanin janyewar dakaru daga Mali

Minsitocin gwamnati daga Faransa da Nijar sun gana a jiya Juma’a a daidai lokacin da dakarun Faransa ke  sake fasalin ayyukansu a yankin Sahel biyo bayan shirin janyewa daga Mali.

Ministar harkokin wajen Faransa  Catherine Colonna, da ministan tsaron Nijar,  Alkassoum Indatou, a ranar 15 ga watan Yuli a Yamai.
Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna, da ministan tsaron Nijar, Alkassoum Indatou, a ranar 15 ga watan Yuli a Yamai. AFP - BERTRAND GUAY
Talla

Ministar harkokin waje Catherine Colonna da ministan tsaro Sebastien Lecornu sun isa Niamey, babban birnin Nijar ne a ranar Alhamis.

An yi wannan ganawa ce a yayin da dakarun Faransa ke kokarin kammala janyewa daga Mali, inda suke hangen kafa sansani a Nijar, a matsayinta ta kasar da ke kan gaba a yakin da ake da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.

Gabanin balaguron, ministar harkokin wajen Faransa Colonna, ta shaida wa ‘yan majalisar dokokin kasar cewa, koma baya da ake samu a  yankin yammacin Afrika abin takaici ne, tana mai nuni da juye juyen mulki da aka samu a yankin a baya bayan nan.

Sai dai ta ce duk da haka, da ma janyewa  da za ta yi daga Mali, Faransa za ta ci gaba da taimaka wa sojojin yammacin Afrika a wajen yaki da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Nijar ta sha radadin ayyukan ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi tun da suka fara kai hare hare a yankin arewacin Mali a shekarar 2012, suka kuma bazu zuwa sauran kasashe makwafta.

Dimbim fararen hula ne aka kashe a fadin yankin Sahel, kuma fiye da miliyan 2 suka tsere daga gidajensu.

Nijar na fama da wannan matsala ta ‘yan ta’adda a iyakokin kasarta da Burkina Faso daga yammaci, da kuma kudu maso gabashin kasar a iyakarta da Najeriya.

Yanzu haka ta karbi ‘yan gudun hijira daga Burkina Faso, Mali da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.