Isa ga babban shafi

Chadi da Nijar sun sha alwashin farfado da rundunar yaki da ta'addanci

Shugabannin kasashen Chadi da Nijaar sun sha alwashin farfado da kungiyar yaki da ta’addanci na kasashen yankin Sahel don karfafa yaki da mayaka masu ikirarin jihadi, bayan janyewar Mali daga kungiyar G5 Sahel.

Shugaban jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum tare da takwaransa na Chadi Mohamed Kaka Idris Deby, yayin ziyara a Ndajamena. 13/07/22.
Shugaban jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum tare da takwaransa na Chadi Mohamed Kaka Idris Deby, yayin ziyara a Ndajamena. 13/07/22. © Presidence du Niger
Talla

Sai dai shugaban Nijar Bazoum Mohamed wanda ya yi wata tattaunawa da jagoran gwamnatin sojin Chadi Mahammat Idriss Deby a N'Djamena, ya yi kame kame a game da tamabayar da aka mai  kan dawowar dakarun Faransa.

Bayan shekaru 9 da aka shafe ana yaki da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi a Mali, Faransa za ta janye  dakarunta tare da rage irin rawar da take takawa a yankin Sahel biyo bayan rashin jituwa da sojojin da suka yi juyin mulki a Mali.

Janyewar Mali

A watan Mayu ne Mali ta sanar da aniyarta ta fita daga kungiyar G5 Sahel, wanda aka kafa a shekarar 2014, kuma ta yi aiki sau da kafa da dakarun Barkhane na Faransa don dakile kungiyoyi ‘yan ta’adda da dama da ke nnosawa kudacin kasar.

Sama da mutane dubu 2 ne  aka kashe a Mali, Nijar da Burkina Faso tun farko wannan shekarar, lamarin da ya sa shugaba Bazoum ya ce akwai sauran aiki a gaban kungiyar G5 Sahel.

Janar Mahamat Idriss Deby wanda ya dare karagar mulki bayan mutuwar mahaifinsa, ya ce ya ji takaicin barin Mali wannan kungiya ta G5  Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.