Isa ga babban shafi

Bazoum ya tattauna matsalolin tsaro da wani babban kwamandan sojin Amurka

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya gana da kwamandan sojin Amurka dake kula da nahiyar Afirka, Janar Stephen Townsend dangane da batun tsaron kasar da kuma yankin Sahel.

Shugaban jamhuriyar Nijar yayin karbar bakwacin babban kwamandan sojin Amurka a Afiirka Janar Stephen Townsend ranar 28 ga watan Yunin 2022 a fadar gwamnatin kasar.
Shugaban jamhuriyar Nijar yayin karbar bakwacin babban kwamandan sojin Amurka a Afiirka Janar Stephen Townsend ranar 28 ga watan Yunin 2022 a fadar gwamnatin kasar. © Presidence du Niger
Talla

Ganawar da shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya yi da kwamandan rundunar sojin Amurka dake kula da nahiyar Afirka, Janar Stephen Townsend ta mayar da hankali akan batutuwa guda 4 da suka shafi diflomaisya da Ci gaba da Dimokiradiya da kuma tsaro.

Fadar shugaban Nijar ta ruwaito Janar Townsend bayan ganawar yana yiwa manema labarai bayanin cewar sun tattauna halin da ake ciki dangane da matsalar tsaron Jamhuriyar Nijar da kuma Yankin Sahel gaba daya.

Townsend wanda ya bayyana Jamhuriyar Nijar a matsayin babbar kawar Amurka, yace sun duna bangarorin da ya dace kasar sa ta taimakawa Nijar domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabe ta.

Hafsan sojin ya bayyana farin cikin sa akan yadda manufofin bangarorin biyu suka yi kama da juna akan matsalar tsaro, inda yake cewa ba hurumin su bane gudanar da aikin soji a Nijar, sai dai hurumin su ne su taimakawa sojojin Nijar wajen ganin sun sauke nauyin dake kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.