Isa ga babban shafi

Kotu a Mali ta fitar da sammacin kama tsoffin ministoci

Kotun kolin kasar Mali ta fitar da sammacin kasa da kasa don cafke wasu manyan jami’an tsohuwar gwamnatin kasar da ke zaune a ketare, wadanda mahukunta ke zargi da aikata laifuka daban daban.

shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita.
shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita. © AFP
Talla

Sanarwar da aka fitar a wannan juma’a ta bayyana cewa uku daga cikin mutanen hudu dai tsoffin ministoci ne wadanda ake zargi da hannu, wajen yin sama da fada da milyoyin kudaden da aka ware domin saya wa jami’an tsaron kasar makamai.

A shekarar 2015 ne gwamnatin kasar, ta kulla yarjejeniyar cinikin makamai da kuma motocin yaki masu sulke da wani kamfani mai suna Paramount da ke Afirka ta Kudu a kan kudi dala milyan 60 wato lokacin da kasar ke karkashin mulkin marigayi Ibrahim Boubacar Keita.

Mutanen hudu dai su ne tsoffin ministocin kudi Boubou Cisse da Mamadou Igor Diarra, sai tsohon ministan tsaro Tieman Hubert Coulibaly da kuma tsohon shugaban bankin BMS Babaly Bah da yanzu haka ke zaune a makociyar kasar Cote d’Ivoire.

A watan Maris din da ya gabata ne, tsohon firaminista kasar a lokacin mulkin Keita, wato Soumeylou Boube Maiga ya mutu a lokacin da yake tsare a hannun mahukuntan kasar da ke zargin sa da wawashe dukiyar al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.