Isa ga babban shafi

Morocco ta kama hanyar sasanta rikicinta da Algeria

Sarkin Muhammad na 6 ya bayyana fatar ganin Morocco ta dawo da huldar diflomasiyyar da ke tsakaninta da makwabciyarta Algeria bayan samun baraka tsakanin kasashen biyu shekara guda da ta gabata.

Tutocin Algeria da Morocco
Tutocin Algeria da Morocco AFP - RYAD KRAMDI,FADEL SENNA
Talla

A jawabinsa na bikin cika shekaru 20 kan mulki, Sarki Mohammad na Morocco ya ce, yana fatan Rabat da Algeria su dawo da kakkarfar huldar diflomasiyya a tsakaninsu kamar yadda suke a baya, gabanin samun baraka a bara.

Sarki Muhammad na 6 ya bayyana cewa, baya tunanin rikicin iyakar da ke tsakanin kasashen biyu ya hana su dawo da hulda tare da fahimtar juna ga kasashen biyu da ya bayyana a ‘yan uwan juna.

Cikin jawabin nasa Sarki Muhammad na 6 ya roki al’ummar Morocco su dauki al’ummar Algeria a matsayin ‘yan uwansu tare da sadaukarwa gare su baya ga taimakon su ta kowacce fuska.

Kasashen biyu na yankin Maghreb na fuskantar tsamin alaka ne tun bayan da Algeria ta goyi bayan ballewar yankin yammacin Sahara ko kuma Polisario da ke neman ‘yancin kai daga Morocco, dalilin da ya sanya Rabat katse hulda da Algerian a watan Agustan 2021 bisa zargin da taimakon ‘yan awaren.

Yankin na yammacin Sahara da Spain ta yi wa mulkin mallaka har zuwa yanzu baya cikin yankunan da Majalisar Dinkin Duniya ke kallo a matsayin masu kwarya-kwaryar ‘yanci yayin da fiye da kashi 80 na yankin ke karkashin ikon Morocco tun shekarun 1970 ko da yake suna fatan Majalisar Dinkin Duniya ta ba su damar zaben raba gardama lamarin da Algeria ta goyi.

Algeria dai ta kwatanta halin da yankin ke ciki da halin da Falasdinu ke ciki batun da ya bai yi wa Rabat dadi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.