Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Uganda ya karu zuwa 22

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a birnin Mbale na gabashin kasar Uganda ya kai 22, ciki har da tawagar wasu masu zuwa gidan biki da lamarin ya ritsa da su a cikin wata karamar motar bas, a cewar ‘yan sanda.

Zuwa yanzu ambaliyar ta kashe mutane 22 yayinda wasu 10 ke kwance a asibiti.
Zuwa yanzu ambaliyar ta kashe mutane 22 yayinda wasu 10 ke kwance a asibiti. AFP PHOTO/ Peter BUSOMOKE
Talla

Wasu koguna biyu ne suka cika suka tumbatsa a karshen makon da ya gabata bayan wani ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya, wanda ya haddasa zaftarewar kasa da ya yi  dimbim barna, ya kuma tilastawa mutane da dama tserewa daga muhallansu.

Rahotanni sun ce yanzu haka tawagar Sojoji da hadin gwiwar ‘yan sanda da kuma jami’an agaji na kungiyar Red Cross na ci gaba da laluben wadanda suka bace a ambaliyar.

Akwai dai bayanan da ke nuna cewa tarin mutane  yanzu haka sun makare a baraguzan gine-gine da suka rushe.

Alkaluman da gwamnati ta bayar ta ce akwai mutane 10 da ke cikin mawuyacin hali a asibiti baya ga gawar mutum 22 da aka gano amma har yanzu akwai wadanda suka yi batan dabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.