An fara taron sassanta 'yan kasar Chadi a N'Djamena
A yau Asabar ake bude tattaunawar sassanta yan kasar Chadi mai cike da rudani tsakanin 'yan adawa, kungiyoyin farraren hula da shugabanin kungiyoyin yan tawaye da wakilan gwamnatin mulkin soja na. Taron da ake kyautata zaton zai taimaka don shifuda sabon babe na shirya mika mulki da kuma ba da damar gudanar da zabuka a karkashin turbar dimokuradiyya. .
Wallafawa ranar:
Mahamat Idriss Déby Itno, wanda ya hau kan karagar mulki a watan Afrilun 2021 bayan rasuwar mahaifinsa Idriss Deby, wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 30, ya yi alkawarin shirya wanan tattaunawa tare da kasanceewar dukkanin 'yan adawa don ba da damar dawo da mulki ga farar hula, a cikin watanni 18.
Wakilai 1,400, mambobin kungiyoyin kwadago, jam'iyyun siyasa da na majalisar sojin kasar, za su yi taron na kwanaki 21, a N'Djamena babban birnin kasar, don tattauna batun sake fasalin hukumomi da sabon kundin tsarin mulkin kasar ta Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu