Isa ga babban shafi

Manyan 'yan tawayen Chadi sun koma kasar bayan shekaru suna gudun hijira

Manyan shuwagabanin yan tawayen Tchadi da suka share tsawon shekaru suna zaman gudun hijira a ketare sakamakon yunkurin da suka yi na kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Idriss Déby Itno, ciki har da Timan Erdimi da Mahamat Nouri, sun koma N'Djamen, babban birnin kasar.

Shugaban gwamnatin sojin Chadi kenan, Idris Deby
Shugaban gwamnatin sojin Chadi kenan, Idris Deby © theguardian
Talla

Timan Erdimi, da ya kasance shugaban kungiyar yan tawayen, da ayarinsa ya dirarwa birnin Ndjamen a 2019 an dakatar da shi ne sakamakon kai daukin jiragen saman Faransa, ya sauka a filin jirgin saman N'Djamena inda ya samu tarba daga wasu makusantansa sama da 50 kamar yadda AFP ya sanar.

Erdimi zai kasance daga cikin manyan masu jawabi a taron tattaunawa na kasa da za a bude a N'Djamena ranar Asabar.

Taron wanda shugaban mulkin sojan kasar Janar Mahamat Idriss Deby ya kirkira, zai hada wakilai 1,400 daga gwamnatin soja, kungiyoyin farar hula, jam'iyyun adawa, kungiyoyin kwadago da kungiyoyin 'yan tawaye.

Deby ya yaba da hakan a matsayin wata dama ta sasantawa a kasar da ta samu rarrabuwar kawuna, inda ya bude hanyar gudanar da zaben mulkin dimokuradiyya a cikin watanni 18 da sojoji suka karbe ikon kasar.

Ya karbi mulki a watan Afrilun bara yana dan shekara 37 kacal bayan da aka kashe mahaifinsa wanda ya yi mulki na tsawon shekaru 30 a wani farmaki da sojoji suka kai wa ‘yan tawaye.

Kusan kungiyoyi 40 ne suka rattaba hannu a ranar 8 ga Agusta kan wata yarjejeniyar, tsagaita wuta da kuma ba da tabbacin warware rikicin da ke faruwa tsakanin bangarorin da bas aga maciji da juna.

Kungiyar ‘yan tawayen ta UFR, na daya daga cikin wadanda suka rattaba hannun, an kiyasta cewa tana da daruruwan mayaka, wadanda ke da sansani a kudancin Libya da arewacin kasar Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.